Messi ya zura kwallo na 700

Dan wasan Barcelona Lionel Messi
Dan wasan Barcelona Lionel Messi REUTERS/Waleed Ali

Lionel Messi yaci kwallo na 700 a rayuwarsa ta tamola, bayan da ya samu bugun fenariti a wasan La liga da Barcelona ta karbi bakwancin Atletico Madrid jiya a Camp Nou, inda aka tashi 2-2.

Talla

Kwallo na 700 da Messi ya zura a wasan na ranar Talata, shine kuma na 630 da yaciwa Barcelona a wasa 724 da ya buga mata, kuma Finaretin na jiya ya shiga tarihin jerin bugun Finareti da dan wasan ya saba yi, wato Panenka.( wanda zakaga ba’a buga kwallo gefen hagu ko dama ba kamar yadda aka saba).

Lokacin da Messi ya ci Kwallon yasa Barcelona tana cin wasa da ci 2 da 1, kafin daga bisani Atletico Madrid ta barke aka tashi wasa ci 2-2, lamarin da ya sake barin ta amatsayi na biyu a jerin teburin gasar, wato har yanzu abokiyar adawarta Read Madrid ke jan ragamar teburin da rattan maki 1 kachal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.