Turai-Coronavirus

Turai ta bude iyakokinta ga bakin kasashe 15

A karon farko tun tsakiyar watan Maris, kungiyar tarayyar Turai ta bude iyakokinta ga baki daga kasashe 15, to sai dai babu Amurka ciki, sakamakon yadda annobar coronavirus ke cigaba da halaka dubban rayuka a kasar.

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Photo: Kenzo Tribouillard/AFP
Talla

Daga cikin kasashen da kungiyar tarayyar Turan ta budewa iyakokinta akwai Algeria, Morocco, Australia, Korea ta Kudu, Japan, Rwanda da Canada, sai kuma China wadda kungiyar ta EU ta gindayawa sharadin cewar dole ta baiwa baki daga gareta damar shiga kasar, kafin itama ta shiga sahun kasashen da nahiyar Turan za ta budewa iyaka.

Kasashen Amurka, Brazil da kuma Rasha dai basa cikin wadanda kungiyar ta EU ta budewa iyaka, sakamakon yadda adadin rayukan da annobar coronavirus ke lakumewa ke dada hauhauwa a maimakon saukin da aka samu a baya.

A Amurka Anthony Fauci, babban mashawarcin gwamnatin kasar kan coronavirus  ya yi gargadin cewar gwamnatin Amurka na tafka kura-kurai wajen kokarin yakar annobar coronavirus, kura-kuran da masanin cutukan ke cewa ka iya kara yawan masu kamuwa da cutar kowacce rana akalla dubu 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI