Turai

'Yansandan Turai sun kwace kamfanin layin sadarwar kungiyar ta'addanci

Wasu 'yansandan Turai a Brussels.
Wasu 'yansandan Turai a Brussels. OLIVIER GOUALLEC / BELGA / AFP

Rundunar ‘yansandan Turai ta sanar katse wani layin sadarwar ‘yan ta’adda da suke amfani da shi wajen tsara yadda za su kai mabanbantan farmaki, aikata kisan kai da kuma safarar miyagun kwayoyi a Nahiyar.

Talla

Tun farko ‘yansandan Faransa da na Netherland ne suka fara bibiyar layin ‘yan ta’addan mallakin kamfanin Encrochat wanda ya kai ga kamen mutane fiye da 100 dukkanninsu masu hannu a ko dai ayyukan ta’addanci ko na tsageranci ko kuma safarar miyagun kwayoyi da fasakwauri.

Kamfanin na EnroChat dai na sayar da wayoyin hannune da ke dauke da layi na din-din-din, wanda kuma ke bayar da damar bibiya ko kuma kutse ga masu amfani da shi ba tare da saninsu ba.

A cewar Wil van Germert babban daraktan rundunar ‘yansandan ta Turai sun yi nasarar datsar tattaunawar ‘yan ta’addan ne tun cikin watan Yuni wanda ya basu damar gano shirye-shiryensu na farmaki da ma kitsa kisan wasu mutane baya ga shirin shigo da tarin miyagun kwayoyi nahiyar ta Turai.

Tun a watan da ya gabata ne, kamfanin na EncroChat ya aike da sako ga abokanan huldarsa cewa su dakatar ko kuma su yaddar da nau’in wayoyin nasu sakamakon yadda gwamnati ta kwace iko da kamfanin ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatocin kasashen na Turai dais un yi zargin cewa kimanin kashi 90 na masu amfani da nau’in wayar ta EncroChat na da alaka da ayyukan ta’addanci ko tsageru ko kuma masu aikata manyan laifuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.