Kamfanin kera jiragen sama a Turai zai rage ma’aikata
Katafaren kamfanin kera jiragen sama mafi girma a Turai ya ce zai iya rage yawan dubban ma’aikatan da yake shirin sallama da adadin dubu 3 da 500, sai dai bisa sharadin dole gwamnatocin Faransa da Jamus su tallafa.
Wallafawa ranar:
Tun a ranar larabar da ta gabata ne dai kamfanin na Airbus ya bayyana shirinsa na sallamar ma’aikata akalla dubu 15 a sassan duniya, daga cikinsu kuma za a sallami dubu 10 ne a Faransa da Jamus kadai.
Kazalika kamfanin Air France a kasar Faransa ya soma nazari domin neman mafita bayan share dogon lokaci jiragen kamfanin suna kasa sabili da cutar Covid 19.
Kungiyar matuka na kamfanin Air France na fatan za a cimma mafita da shugabanin kamfanin ba tareda an fuskanci sallamar dubban ma’aikata ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu