Coronavirus

Za a binciki tsohon Fira Ministan Faransa kan jagorantar yaki da coronavirus

Masu gabatar da kara a Faransa sun bayyana shirin kaddamar da bincike kan yadda tsohon Fira Ministan kasar Edouard Philippe da mukarrabansa suka aiwatar da shirin yaki da annobar coronavirus.

Tsohon Fira Ministan Faransa Édouard Philippe tare da sabon Fira Minista Jean Castex. 3/7/2020
Tsohon Fira Ministan Faransa Édouard Philippe tare da sabon Fira Minista Jean Castex. 3/7/2020 Ludovic Marin / AFP
Talla

Za a soma binciken ne dai biyo bayan wasu korafe korafe guda 9 da aka gabatar kan tawagar yaki da annobar da tsohon fira ministan na Faransa ya jagoranta, cikinsu har da tsohuwar minister lafiya Agnes Buzyn da kuma ministan lafiyar mai ci Olivier Veran.

Jim kadan bayan kama aiki a ranar Juma'a, sabon Fira Ministan Faransa Jean Castex, yayi gargadin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba kan yaki da annobar coronavirus, la’akari da irin tasirin da ta yi wajen gurgunta tattalin arzikin duniya.

Sabon Fira Ministan na Faransa dai ya taba zama babban jami’I a gwamnatin tsohon shugaba Nicolas Sarkozy, zalika shi ne ya jagoranci tsara yadda kasar ta aiwatar da shirin sassauta dokokin hana walwalar da suka shafe watanni suna aiki don yaki da annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI