Spain-Coronavirus
Sake barkewar cutar corona ya tilasta killace mutane dubu 200 a Spain
Gwamnatin yankin Catalonia dake Spain ta killace akalla mutane dubu 200, biyo bayan sake barkewar cutar coronavirus a garin Lerida, makwanni kalilan bayan saukin da annobar ta yi.
Wallafawa ranar:
Talla
Matakin sake killace dubban mutanen da hukumomin Catalonia suka yi na zuwa ne jim kadan bayan soma hutun ayyuka da makarantu, da kuma bude iyakoki ga baki daga kasashe 12 dake wajen tarayyar Turai da gwamnatin Spain tayi.
Tuni dai Minsitar lafiyar Spain Alba Verges, ta yi shelar haramta taron sama da mutane 10, da kuma dakatar da ziyartar gidajen kula da tsofaffi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu