Faransa

Macron ya cika Majalisar Ministocinsa da masu ra'ayin 'yan mazan jiya

Shugaban Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana fatar gagarumar nasara a zaben kasar da ke tafe cikin shekarar 2022 bayan kafa sabuwar majalisar ministoci da ke tattare da masu ra’ayin ‘yan mazan jiya.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da sabon Firaministan kasar Jean Castex.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da sabon Firaministan kasar Jean Castex. Ludovic MARIN / AFP
Talla

Masharhanta dai na ganin gina sabuwar gwamnatin da masu ra'ayin 'yan mazan  jiyan da yadda shugaba Macron ya dauri aniyar sake daidaita ginshikan tattalin arzikin kasar da suka rankwafa a gaba zai daga martabarsa tare da iya bashi nasara a zaben na 2020.

Bayan koma bayan jam'iyyarsa mai tsaka-tsakin ra’ayin a zabukan da suka gabata, shugaba Macron karkata hankalinsa bangaren jam'iyyun masu rajin kare mahalli wadda ke ci gaba da habaka da kuma ta samu rajin yakar dummar yanayi da nufin  kafa sabuwar gwamnatin da aka jima ana jira.

Kusan dai dukkanin sabin ministocin na Macron sun fito ne daga bangaren jam'iyya mai ra'ayin yan mazan jiya, musaman ma makusanta ga tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy.

Idan aka dauki Firaminista Jean Castex da ake dangantawa da jajirtacen ma'aikaci da ke a labe, an bayyana shi da jami'i mai matukar fikira wajen gudanar da ayyukansa musamman a lokacin da ya rike mukamin mataimakin daraktan fadar shugaba Sarkozy.

Sabuwar Ministar al'adu Rosalyne Bachelot ita ta rike ministan kiwon lafiya a lokacin Sarkozy, yayinda kwararen lauya Eric Dupond-Moretti, ya zama Ministan shari'a.

Gerald Darmanin, tsohon kakakin fadar shugaba Sarkozy yanzu kuma shine mataimakin ministan kudi Bruno Le Maire haka kuma wani tsohon ministan Sarkozy ne aka sake bai wa mukamin ministan cikin gida.

Duk wannan ya nuna karara yadda masu ra'ayin 'yan mazan jiyan makusanta ga Sarcozy suka mamaye sabuwar gwamnatin ta shugaba Macron a cewar masharhanci Pascal Perrineau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI