EU ta kafa asusun tunkarar kalubalen da ficewar Birtaniya zai haifar mata
Shugaban Majalisar Turai Charles Michel ya gabatar da wani gagarumin shirin da zai kai ga kafa asusun euro biliyan 5 da zai magance duk wata matsalar da ka iya tasowa sakamakon ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar.
Wallafawa ranar:
Yayin da ya ke gabatar da shirin yau wanda ake saran shugabannin kasashen Turai suyi mahawara akai makon gobe, Charles Michel ya bayyana ficewar Birtaniya daga kungiyar a matsayin wani babban kalubale da ya shafi kowa, wanda ya zama wajibi a samar da irin wannan asusu euro biliyan 5 domin shawo kan duk wata matsalar da ka iya bijirowa.
Jami’in ya ce ficewar Birtaniya ko da yarjejeniya ko kuma babu zai haifar da matsalla ga kasashen da ke nahiyar Turai, wanda ya ce daukar wannan mataki zai bai wa kungiyar damar shiryawa domin tinkarar duk wani abinda zai biyo baya.
Yanzu haka Birtaniya da kungiyar Turai na cigaba da tattaunawa a tsakanin su, kuma Michel ya ce nan da zuwa karshen watan Agusta ko Satumba suna saran samun haske dangane da yadda tattaunawar ke gudana da kuma nasarar da ake samu.
Rahotanni sun ce Ireland ce za ta fi jin radadin ficewar Birtaniya daga kungiyar, sai kuma Belgium da arewacin Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu