Bosnia

Musulmi na alhinin cika shekaru 25 da yi musu kisan kare dangi a Bosnia

Yau al’ummar Musulmin Bosnia sun yi tarukan alhinin tuna kisan gillar da aka yiwa ‘yan uwansu shekaru 25 da suka gabata da aka yiwa lakabi da ‘kisan Srebrenica’, kisa mafi muni da aka taba gani a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Wata mata yayin addu'a ga 'yan uwanta Musulmi da aka yiwa kisan kare dangi a garin Srebrenica dake Mexico shekaru 25 da suka gabata.
Wata mata yayin addu'a ga 'yan uwanta Musulmi da aka yiwa kisan kare dangi a garin Srebrenica dake Mexico shekaru 25 da suka gabata. ELVIS BARUKCIC AFP/File
Talla

Masu juyayin mutuwar da dama sun bijirewa matakan da hukumomi suka dauka domin dakile yaduwar cutar coronavirus domin halartar bikin tuna mutanen da aka kashe da kuma birne Karin wasu mutane 9 da aka gano gawarwakin su.

A ranar 11 ga watan Yulin shekarar 1995 sojojin Sabiya suka kasha Musulmi maza manya da kanana sama da 8,000 a cikin kwanaki kadan, kisan da ya girgiza duniya.

Sehad Hasanovic mai shekaru 27 na daya daga cikin yan uwa akalla 3,000 da suka halarci bikin na yau, yace abin takaici ne ga wasu suna kira iyayen su kai kuma baka da wanda zaka kira.

Kotunan Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun bayyana kisan Srebrenica a matsayin kisan kare dangi bayan yakin da akayi tsakanin Kroshawa da Sabiyawa Musulmi wanda ya lakume rayukan mutane sama da 100,000.

Ya zuwa yanzu an iya gano gawarwakin mutanen da aka kashe 6,900 daga cikin manyan kaburbura 80 da aka birne su.

Tuni aka yankewa Janar Ratko Mladic da Radovan Karadzic hukukcin daurin rai da rai a kotun duniya saboda rawar da suka taka wajen aikata kisan kare dangin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI