Italiya

Italiya za ta rage yawan 'yan majalisar dokokinta

Italiya ta sanya watan Satumba mai zuwa a matsayin lokacin da za ta gudanar da kuri’ar raba gardama domin rage yawan ‘yan Majalisun wakilai da na Dattawan kasar.

Firaministan Italiya Giuseppe Conte.
Firaministan Italiya Giuseppe Conte. REUTERS/Remo Casilli
Talla

Ana sa ran kasar ta rage yawan ‘yan majalisun wakilai daga 945 zuwa 600, yayin da ‘yan Majalisun Dattawa zasu ragu daga 630 zuwa 400, abin da zai taimaka wa kasar ceto euro miliyan 500 da ake biyan su a kowanne zango da suke zama.

Da dai, an shirya gudanar da zaben raba gardamar ne a watan Maris, yayin da zaben shiyya kuma zai gudana a watan Mayu amma annobar coronavirus ta dakatar da shirin.

Akasarin jam’iyyun siyasa na kasar sun yi na’am da wannan sauyi da ke tafe, wanda ake sa ran masu kada kuri’a su hatimce shi a ranakun 20 da 21 ga watan Satumba.

Mutane miliyan 21 ne za su kada kuri’a a wannan zaben raba gardama da za a yi yankunan Tuscany, Puglia, Campania, Veneto, Marche da Liguria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI