Amurka-Iran

Trump ya gargadi Iran game da aiwatar da kisa kan masu zanga - zanga

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Iran da kada ta kuskura ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu 'yan kasar 3 da aka samu da laifin zanga - zangar da aka yi a watan Nuwamba bara.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP
Talla

A sakon da ya aike da twitter, Trump ya ce aiwatar da hukuncin kisan zai aike da mummunan sako ga duniya saboda haka bai dace a yi ba.

Ma’aikatar shari’ar Iran ta ce kotun daukaka kara ta amince da hukuncin kisan saboda laifuffukan da aka aikata lokacin zanga zangar kara farashin mai.

Jaridar Shargh mai da’awar sauyi ta ce mutanen da ke jiran hukuncin sune : Amirhossein Moradi, mai shekaru 26 da yake kasuwancin sayar da wayar hannu, Said Tamjidi, mai shekaru 28 wanda dalibi ne, sai Mohammad Rajabi, mai shekaru 26.

Iran ta zargi ‘yan tsagera masu samun goyon bayan abokan gabanta kamar Amurka, Isra’ila da Saudiyya da kitsa zanga zangar ta shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI