Faransa

An kashe gobarar da ta tashi a dadaddiyar majami'ar birnin Nantes

Wani bangare na majami'ar birnin Nantes da gobara ta tashi.
Wani bangare na majami'ar birnin Nantes da gobara ta tashi. SEBASTIEN SALOM-GOMIS / AFP

Gobara ta tashi a wata majami’a dake birnin Nantes a yammacin Faransa a Asabar din nan, amma masu aikin kashe gobara sun ci karfin wutar cikin ‘yan sa’o’i.

Talla

Hukumomi sun ce gobarar ta yi barna a majami’ar, kuma a ba mamaki wasu sassanta su fadi, sai dai sun kara da cewa ta’adin bai kai wadda gobara ta yi a majami’ar Notre Dame ta birnin Paris ba.

Da misalin karfe 8 na safiyar yau Asabar ne aka sanar da masu kashe gobara cewa wuta ta tashi a majami’ar Saint Peter da Paul, inda jami’ai kashe kusan 100 suka nufi wajen.

Bayan sa’o’i biyu ne jami’an kashe gobarar suka shawo kan wutar da ta kama ginin majami’ar da aka gina a tsakanin karni na 16 da 19, a cewar babban jami’in kashe gobara na yankin Laurent Ferlay.

Firaminista Jean Castex ya ce zai ziyarci inda lamarin ya auku anjima a Asabar din nan.

Shugaba Emmanuel Macron ya wallafa sakon goyon baya ga jami’an kashe gobara a shafinsa na Twitter, ind ya ce sun sadaukar da rayuwansu yayin ikinsu.

A watan Afrilun shekarar da ta gabata wuta ta tashi a majami’ar Notre Dame da aka gina a karni na 13 a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.