Macron ya taya Amurkawa alhinin mutuwar John Lewis
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon taya Amurkawa da ma duniya baki daya alhinin mutuwar John Lewis fitaccen mai rajin kare hakkin dan adam, da suka yi gwagwarmayar kare hakkin bakaken fata tare da Martin Luther King sama da shekaru 57 da suka gabata.
Wallafawa ranar:
A Juma’ar nan da ta gabata, John Lewis, da ya kasance dan majalisar wakilan Amurka tun daga shekarar 1986 a karkashin jami’iiyar Democrats ya mutu yana da shekaru 80, bayan fama da cutar Kansa.
Lewis wanda ke cikin mutane masu kima a Amurka saboda fice wajen neman daidaito a tsakanin jama’a, ya sha caccakar shugaban Amurka Donald Trump, tun farkon darewarsa kujerar shugabancin kasar, inda ya kauracewa bikin rantsar da shugaban, tare da diga ayar tambaya kan sahihancin nasarar lashe zaben da Trump yayi na 2016, bisa zargin Rasha ta taimaka masa, ta hanyar yin katsalandan a zaben shugabancin na Amurka.
Duk da cewar yana jinyar cutar Kansa, a watan Yunin da ya gabata, marigayi John Lewis yayi tattaki zuwa birnin Washington don bada gudunmawarsa wajen zanga-zangar nuna kyama da cin zarafin da ‘yan sanda ke yiwa bakar fata a Amurka, da ta samo asali bayan mutuwar Gorge Floyd a hannun wasu ‘yan sandan birnin Minneapolis.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu