Jayayya ta hana kasashen Turai cimma matsaya kan Euro biliyan 750
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Waziriyar Jamus Angela Merkel sun bayyana fatar cimma matsaya kan tsarin farfado da kasashen Turai da annobar coronavirus ta yi wa illa.Wannan na zuwa ne a yayin da kasashen na Turai suka shiga rana ta hudu suna gudanar da jerin tattaunawa kan wannan batu a birnin Brussels.
Wallafawa ranar:
A yayin da aka ci gaba da gudanar da tattaunawar mai cin rai, shugaba Macron ya ce, akwai yiwuwar sulhuntawa don cimma matsaya, amma kawo yanzu babu wata yarjejeniya da kasashen suka amince da ita, yayin da shugaban na Faransa ke cewa, zai yi taka-tsan-tsan.
Macron ya kara da cewa, sun gamu da wani yanayi mai cike da wahala kuma babu shakka nan gaba irin wannan yanayin zai sake ta’azzara.
Kalaman na Macron na zuwa ne bayan kasashen na EU 27 sun koma teburin tattaunawa bayan kwashe tsawon yini uku da darare suna doguwar jayayya ba tare da cimma matsaya ba kan kasafta Euro biliyan 750 na farfado da komadar kasashen.
Macron da Merkel ta Jamus da suka kasance shugabanni mafi karfi a Turai, sune suka goyi bayan yarjejeniyar, amma suna fuskantar gagarumar adawa daga Netherlands da wasu kananan kasashen arewacin Turai da ke nuna turjiya duk da cewa, suna da hali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu