Turai

Shugabannin EU sun gaza cimma matsaya kan raba tallafin farfado da tattalin arziki

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai EU, sun shafe kwanaki 3 suna tattaunawa ba a birnin Brussels, ba tare da cimma matsaya kan yadda za su kasafta tallafin euro biliyan 750 don farfado da tattalin arzikinsu da annobar COVID-19 ta durkusar ba.

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Photo: Kenzo Tribouillard/AFP
Talla

Daya daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin kasashen Turan 27 suka tafka muhawara akai shi ne kason da ya kamata kowace kasa ta samu, musamman kasashen da annobar ta COVID-19 ta fi yiwa illa.

Yayin taron dai Firaministan Netherlands Mark Rutt ya ce ya zama dole kasashen na EU su mutunta kudurin farko na bada kaso na musamman ga kasashen da annobar ta coronavirus ta fi yiwa illa, kamar Italiya da Spain, la’akari da yadda matakan killace jama’ar da suka dauka masu tsauri ya durkusar da tattalin arziki, ko da dai bukatar ta sa ba ta samu karbuwa ba.

A nasa bangaren shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bukaci takwarorinsa na Turan da su ajiye san kai a gefe domin ceto tattalin arzikin Nahiyar da annobar coronavirus ta tagayyara, wanda rabon da ya fada cikin irin wannan mawuyacin hali, tun bayan yakin duniya na 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI