Kasashen EU sun cimma jituwa kan rabon kudin farfado da tattalin arziki
Bayan shafe kwanaki 4 cur ana tafka mahawara kan yadda za a rarraba kudin tallafin farfado da tattalin arzikin da coronavirus ta kassara, shugabannin kasashen Turai sun cimma matsaya a safiyar yau Talata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kudaden yuro biliyan 750 wanda ya haddasa rashin fahimtar juna tsakanin kasashen kungiyar 27 musamman masu ra’ayin tsumulmula, an cimma jituwar a safiyar yau ne bayan da Faransa da Hungary suka yi barazanar ficewa daga tattaunawar, yayinda kasashen sakamakon yadda kasashen Holland da Austria suka bayyana tsarin rabon kudin a matsayin mai cike da hadari.
A cewar shugaban majalisar Turai Charles Michel wannan ce jituwa mafi wahala da kasashen 27 suka cimma bayan tattaunawar sa’o’i fiye da 90, sai dai ya yi ikirarin cewa kowanne bangare zai ga alfanun matsayar.
Takaddar bayan taron da EU ta fitar wadda ke da cikakken goyon bayan kasashen Faransa da Jamus, ta aminta da bayar da lamunin makudan kudade tsakanin kasashen kungiyar 27.
Karkashin matsayar da aka cimma kunshin tallafin zai fi fifita kasashen Sapain da Italy wadanda suka wahaltu da annobar ta COVID-19 ta hanayar basu yro biliyan 140 cikin shekaru 6 masu zuwa don farfado da tattalin arzikinsu.
Cimma matsayar dai na matsayin gagarumar nasara ga shugaba Emmanuel Macron na Faransa da ya tsaya kai da fata wajen tabbatauwar shirin baya ga Angela Merkel da ke mara masa baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu