Brazil: Sama da mutane dubu 55 sun kamu da cutar COVID-19 a rana guda

An gano karin sama da mutane dubu 50 da suka kamu da cutar coronavirus cikin rana guda a Brazil.

Makabartar Vila Formosa mafi girma a Brazil dake birnin Sao Paulo, yayin binne dubban mutanen da annobar coronavirus ta halaka a kasar.
Makabartar Vila Formosa mafi girma a Brazil dake birnin Sao Paulo, yayin binne dubban mutanen da annobar coronavirus ta halaka a kasar. REUTERS/Amanda Perobelli
Talla

Ma’aikatar lafiyar Brazil ta ce a jiya Juma’a kadai, karin mutane dubu 55 da 891 suka kamu, yayinda cutar ta kashe dubu 1 da 156 cikin sa’o’I 24.

A jumlace adadin wadanda suka kamu da coronavirus a Brazil yanzu haka ya zarta miliyan 2 da dubu 300, daga cikinsu kuma akalla dubu 85 da 238 sun mutu.

A wani labarin kuma shugaban kasar ta Brazil Jair Bolsonaro ya sanar da warkewa daga cutar ta COVID-19, makwanni biyu bayan kamuwa da ita, inda kuma gwaji har sau 3 ya gwada cutar na nan a jikinsa, tsawon kwanakin 14.

A baya Jair Bolsonaro ya sha yin watsi da barzanar annobar ta COVID-19, wadda ya bayyana ta a matsayin ‘yar mura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI