'Yan sandan Amurka sun sake yin arrangama da masu zanga-zanga
‘Yan sanda a Amurka sun sake yin arrangama da fararen hula yau lahadi a biranen kasar, bayanda dubban mutane suka fito zanga-zanga bayan fusatar da suka yi, da shirin shugaban kasar Donald Trump na aikewa da karin jami’an tsaro zuwa biranen kasar.
Wallafawa ranar:
Trump ya bayyana aniyar aikewa da karin jami’an tsaron ne, ganin yadda zanga-zangar nuna kyama kan cin zarafin fararen hula musamman bakar fata da wasu ‘yan sanda ke yi taki ci taki cinyewa, inda a lokuta da dama fada ke barkewa tsakanin mutane da jami’an tsaro.
Biranen da dubban Amurkawa suka gudanar da zanga-zangar a yau dai sun hada da, Austin, Texas, Louisville, Oakland, Los Angeles da kuma New York, kuma a dukkanin biranen sai da ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan don tarwatsa masu zanga-zangar.
A karshen watan Mayu, karon farko tun bayan yakin duniya na 2 gwamnatin Amurka ta baiwa dakarun sojanta na musamman da a turance ake kira da ‘National Guard’ umarnin maido da doka a wasu biranen kasar da dubban mutane ke zanga-zanga kan kashe wani bakar fata da wani jami’in dan sanda mai suna Derek Chauvin yayi a birnin Minneapolis dake Minnesota.
Yayin sanar da umarnin aikewa da dakarun sojin, gwamnan jihar ta Minnesota Tim Walz yace daukar matakin ya zama dole, la’akari da cewar wasu bata gari sun soma amfani da zanga-zangar kan mutuwar George Floyd wajen tayar da bore da kuma lalata dukiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu