Amurka

Baitulmalin Amurka ya aike wa matattu tallafin corona na sama da dala biyan 1

Baitulmalin Amurka ya aike da kudin da ya kai kusan Dala biliyan guda da rabi ga mutanen da suka mutu a matsayin tallafin annobar COVID-19 cikin kuskure.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Wannan na daga cikin kura kuran da Baitulmalin ya tafka wajen aikewa jama’a kudade domin rage radadin annobar wadda ke cigaba da lakume rayuka.

Tun daga watan Maris da ya gabata, Majalisar dokokin Amurka ta amince da shirin rabawa yan kasar sama da Dala triliyan 2 da rabi domin bunkasa tattalin arzikinsu da ya samu targade sakamakon annobar.

Masu bincike sun ce Baitulmalin ya aikata wannan kuskure ne wajen aikin gaggawa domin ganin mabukata sun samu tallafin ba tare da duba takardun mamata a cikin kasar ba.

Kasar Amurka ce a sahun gaba wajen yawan mutanen da cutar ta kama a duniya da kuma yawan wadanda suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI