Faransa na neman a binciki China kan cin zarafin Musulmi
Faransa ta bada shawarar aika tawagar kasashen duniya karkashin jagorancin hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Xinjiang, dake arewa maso yammacin China, domin gudanar da binciken halin da yan tsirari musulmin ouïghoure ke ciki.
Wallafawa ranar:
A lokacin da yake tsokaci kan halin da al’ummar musulmin da ake tsare da su a wasu sansanonin yankin Ouïghours na kasar China ke ciki, Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya sanar da Majalisar Dokokin kasar ta Faransa cewa, a yankin ana aikata abinda ya sabawa tsarin da babbar yarjejeniyar dunuiya kan kare hakkin dan adam ta tanada, inda Chinar ke ci gaba da tsare musulmi a gidajen kurkuku da kuma hanasu fita daga gidajensu, tilasta masu ayukan karfi ko kuma hanasu gudanar da wasu fannoni na addininsu na musulunci.
Ko a makon da ya gabata a gaban Majalisar Dokokin ministan Le Drian ya bayyana abinda ke faruwa na cin mutuncin yan tsirarun musulmi a wannan yanki na kasar China da zama abinda duniya ba za ta taba amince da shi ba, inda ya bukaci aika tawagar kasashen duniya mai cin gashin kanta a yankin na Xinjiang domin gudanar da bincike.
A lokacin da take mayar da martani kan wannan furci na Farnsa, China ba bayyana zargin da zama na karya tsagoronta.
Kakakin fadar gwamnatin Pekin ya ce, siyasar kasar a yankin Xinjiang ba ta takurawa gungunan al’ummar dake rayuwa a yankin ba ce, inda ya ce siyasar kasarsa a yankin ba ta take hakkin dan adam ko takaita yancin adini ba ce, amma ta na yaki da ayukan taaddanci da kuma yinkurin yan aware a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu