Kimiya

NASA ta harba kumbon 'yan sama jannati zuwa duniyar Mars

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, ta harba kumbonta mai suna Atlas 5, dauke da jirgin ‘yan sama jannati zuwa Mars, domin gudanar da binciken gano ko an taba rayuwa a duniyar.

Kumbon Atlas 5 da hukumar binciken sararin samaniya NASA, ta harba zuwa duniyar Mars. 30/7/2020.
Kumbon Atlas 5 da hukumar binciken sararin samaniya NASA, ta harba zuwa duniyar Mars. 30/7/2020. REUTERS/Joe Skipper
Talla

Ana sa ran jirgin na ‘yan sama Jannati ya isa Mars a watan Fabarairu na shekarar 2021, inda zai ajiya na’urorin bincike masu sarrafa kansu don gudanar da binciken kimiyya, don gano ko dan Adam zai iya rayuwa a duniyar ta Mars mai makwabtaka da duniyar da muke.

Kumbon na NASA ya tunkari duniyar ta Mars ce cikin tsala gudun kilomita dubu 40 a sa'a 1.

Hukumar NASA ta tsara jirgin na ‘yan sama Jannatin zai sauka a gaban wani makeken rami mai zurfin mita 250, wanda binciken kimiyya ya nuna cewar ramin tabki da ya wanzu shekaru biliyan 3 da miliyan 500 da suka gabata, inda na’urorin binciken za su yi kokarin gano cewar ko an taba samun rayuwa cikin tsohon tabkin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI