Amurka

'Yan majalisun Amurka sun yi fatali da shawarar Trump kan neman jinkirta zabe

‘Yan majalisun dokokin Amurka daga jam’iyyun Republican da Democrats, sun yi watsi da shawarar shugaba Donald Trump ta neman jimkirta zabukan kasar, ciki har da na shugaban kasa, dake tafe a ranar 3 ga watan Nuwamba.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria
Talla

A ranar Alhamis ta shafinsa na twitter Trump ya bada shawarar dage zabukan, bisa hujjojin fama da annobar coronavirus, da kuma fargabar tafka magudi idan aka yi amfani da tsarin kada kuri’u ta sakwannin mail a maimakon zuwa rumfunan zabe, don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Trump wanda wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna abokin hamayyarsa Joe Biden ke kan gaba wajen samun karbuwa ga jama’a, ya ce ba zai aminta da sahihancin sakamakon zaben da za a bi tsarin kada kuri’a ta mail ba, saboda abu ne mai sauki a tafka magudi.

Kalaman shugaba Trump a twitter sun zo ne a daidai lokacin da Amurka ke fuskantar kalabale ta fuskoki da dama, da suka kunshi fama da annobar coronavirus da ta halaka sama da mutane dubu 150 a kasar, karyewar tattalin arziki, da kuma zanga-zangar dubban jama’a a fadin kasar, kan cin zarafin fararen hula musamman bakar fata, da wasu ‘yan sandan kasar ta Amurka ke yi.

A ranar Alhamis 30 ga watan Yuli, kididdigar masana ta nuna cewar tattalin arzikin Amurka ta durkushe da akalla kashi 32.9 a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI