Amurka

Amurka ta bayyana shakku kan ingancin rigakafin corona na Rasha da China

Shugaban cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Amurka, Dakta Anthony Fauci
Shugaban cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Amurka, Dakta Anthony Fauci Kevin Dietsch-Pool/Getty Images

Amurka tace abu ne mawuyaci tayi amfani da magungunan rikafin cutar COVID-19 da kasashen China da Rasha ke kokarin samarwa a nan kusa.

Talla

Kalaman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanoni hada magunguna a kasashe daban daban suka dukufa wajen lalaubo maganin annobar ta COVID-19, da kawo yanzu ta halaka sama da mutane dubu 680 a fadin duniya, watanni 6 bayan bullarta daga kasar China.

Yanzu haka dai kamfanonin China da dama ne ke kan gaba a kokarin gaggauta samar da maganin cutar ta coronavirus.

Sai dai shugaban cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Amurka, Anthony Fauci yace zai wahala su karbi magungunan da suka fito daga China da Rasha, saboda rashin gamsuwa da matakan kasashen wajen gwaji, kafin soma amfani da su kan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI