Jamus

COVID-19: Dubban mutane na zanga-zangar adawa da matakan takaita walwala a Berlin

Dubban Jamusawa yayin zanga-zangar adawa da matakan hana walwala don yakar annobar coronavirus.
Dubban Jamusawa yayin zanga-zangar adawa da matakan hana walwala don yakar annobar coronavirus. AFP/John MACDOUGALL

Dubban mutane sun fantsama kan titunan Berlin babban birnin Jamus, domin zanga-zanga neman tilastawa gwamnati janye dokokin takaita walwalar da ta kafa domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

Rundunar ‘yan sandan Jamus tace adadin masu zanga-zangar a yau asabar ya kai dubu 15.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP yace kalilan daga masu zanga-zangar ne suka sanya takunkuman rufe baki da hanci, da kuma kiyaye bada tazara.

Da dama daga cikin masu zanga-zangar dai na kallon barkewar annobar COVID-19 a matsayin wani shiryayyen al'amari.

Hakan ta sanya ‘yan sandan na Jamus shigar da karar wadanda ke jagorantar zanga-zangar gaba kotu, bisa tuhumarsu da gazawa wajen tabbatar da bin dokokin kiyaye lafiyar jama’a yayin gangamin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI