Dokar tilasta amfani da kellen rufe hanci da baki ta soma aiki a Faransa

Franministan Faransa Jean Castex da wasu mukarrabansa sanye da kellen rufe hanci da baki
Franministan Faransa Jean Castex da wasu mukarrabansa sanye da kellen rufe hanci da baki DENIS CHARLET / AFP

Fraministan Faransa Jean Castex ya bukaci al’ummar kasar da su ci gaba da rike shirinsu dangane da annobar Covid-19, domin samun damar kaucewa sake bullar ta a karo na biyu cikin kasar.

Talla

Jean Castex ya bayyana hakan ne a birnin Lille dake arewacin Faransa inda daga yanzu saka takunkumin baki da hanci ya zama wajibi a wasu wuraren haduwar jama’a, a rufe suke ko a bude dake ko ina cikin fadin kasar.

Castex Ya ce kwayar cutar bata tafi hutu ba haka mu ma, ya kamata mu kare kanmu daga barin kamuwa da wannan cuta, ba tare da dakatar da fannonin tattalin ariziki da na rayuwar jama’a ta hanyar kaucewa sake komawa babbar killacewar al’umma.

Ya ce a wasu yankuna na Faransa an lura da samun karuwar mutanen dake kamuwa da annobar a cikin hanzari al’amarin da zai kaimu ga kasancewa cikin taka tsantsa a cewar Jean Castex da yaki amsa tambayoyin yan jaridu.

Ya yaba da aikin gwajin cutar da aka yi a kan mutane dubu 14.000 a yankin na Lille da ke fuskantar barazanar kara samun yawan masu kamuwa da annobar ta Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI