Amurka

Yawan mata bakar fata dake takarar zuwa majalisar dokokin Amurka ya karu

Adadin mata bakar fata mafi yawa a tarihi na neman shiga majalisar dokokin Amurka
Adadin mata bakar fata mafi yawa a tarihi na neman shiga majalisar dokokin Amurka Getty Images

Rahotanni daga Amurka sun ce yawan mata bakake dake neman takarar zuwa mjalisar dokokin kasar ya karu zuwa adadin ba a gani ba a tarihi.

Talla

Wannan na zuwa yayinda Amurkan ke fama da annobar coronavirus, da kididdiga ta nuna tafi halaka bakaken fatar kasar, sai kuma boren dubban jama’a kan cin zalin da ‘yan sandan ke yiwa bakar fatar.

Sakamakon binciken da cibiyar kare ‘yancin mata da karfafa musu gwiwar shiga siyasa dake Amurka CAWP ta fitar a baya bayan nan, ya nuna cewar akalla mata bakake fata 122 ne suka gabatar da takardun tsayawa takarar neman zuwa majalisun dokokin kasar, a zaben dake tafe a karshen shekara, sabanin adadin 48 da aka gani a shekaru 8 da suka gabata.

Wata kididdigar ta daban ta nuna cewar yawan mata bakaken fata a Amurka ya kai kusan kashi 8 cikin 100, daga cikinsu kuma kashi 4.3 ke wakilci a majalisar dokokin kasar, zalika kalilan daga cikinsu ke rike da manyan mukaman siyasa da na gwamnati.

Sai dai bincike ya nuna matan bakaken fata sun dara kowane rukuni ko jinsin Amurkawa shiga a dama da su cikin harkokin siyasa, ciki har da kada kuri’u.

Tarihi a Amurkan dai ya nuna cewar, mata bakar fata sun fi lashe zabuka a yankunan da jinsinsu yafi rinjaye, sai dai a bana bakaken da dama sun tsaya takara a yankunan da fararen fata suka fi rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.