Amnesty ta bukaci binciken kasa da kasa kan fashe fashen Lebanon

Hassan Diab, Firaministan Lebanon.
Hassan Diab, Firaministan Lebanon. REUTERS/Mohamed Azakir

Jami’an ceto da kyayyakin agaji, da suka hada da asibitocin tafi da gidanka daga sassan duniya, na ci gaba da kwarara zuwa Lebanon, bayan tagwayen fashe fashe a tashar ruwan dake Bierut, da suka ragargaza kusan rabin birnin, haddasa asarar rayuka, jikkatar dubbai da kuma rasa dimbin dukiya.

Talla

Yayinda Lebanon ke ci gaba da samun taimakon, gwamnatin kasar ta baiwa kwamitin da ta kafa wa’adin kwanaki 4 kacal, da ya gudanar da bincike tare da zakulo duk wani mai hannu cikin tagwayen fashe-fashen a tashar ruwan dake Beirut, wanda jami’ai a kasar suka ce sinadaran ammonium da ake hada taki ne na akalla ton dubu 2 da 750 suka haddasa, lamarin da yayi sanadin ragargaza kusan rabin birnin, halaka sama da mutane 135 da kuma jikkata wasu akalla dubu 5, baya ga bacewar da dama.

Sai dai a nata gefen kungiyar kare hakki ta Human Rights Watch ta bukaci gudanar da bincike na kasa da kasa kan tagwayen fashe-fashen na Lebanon, kamar yadda ake ta kirayen kirayen yin hakan, domin matakin ne kawai zai bada damar yin adalci wajen binciken.

Binciken sharar fage ya nuna cewar an share akalla shekaru 6 ana sakaci wajen kula da sinadarai masu fashewar dake makare a rumbunan tashar ruwan birnin na Beirut.

Dubban ‘yan Lebanon na ci gaba da bayyana fusata da shugabannin kasar, bisa sakacin da ya kai ga tarwatsewar dubban ton na ababen fashewar a Bierut.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.