Sauyin yanayi zai haifar da mummunar fari a Turai - rahoto

Fari na daf da addabar Turai saboda sauyin yanayi.
Fari na daf da addabar Turai saboda sauyin yanayi. Reuters

Wani Binciken masana yace muddin kasashen dake tsakiyar Turai suka gaza wajen daukar matakan rage fitar da sinadarin dake gurbata muhalli kamar yadda aka gani a shekarar 2018 da 2019, matsalar na iya haifar da fari mai tsanani a Turai.

Talla

Rahotan binciken da masana kimiya suka yi, ya ce an samu shekaru 5 mafi zafi tsakanin shekarar 2014 zuwa 2019, amma zafin da aka gani na shekaru biyu da suka wuce ya haifar da fari a tsakiyar nahiyar Turai.

Sakamakon binciken da aka wallafa a Mujallar Kimiya ta ‘Nature Journal Scientific Reports, ya ce masana a Jamus da Jamhuriyar Czech sun yi amfani da alkaluman da aka tattara na ma’aunin zafi tun daga shekarar 1766 domin kamala binciken su.

Rohini Kumar, daya daga cikin wadanda suka jagoranci binciken ya ce sakamakon nazarin da suka yi ya nuna cewar gurbata muhallin na iya ribanya farin da aka gani a tsakiyar Turai daga sau biyu zuwa har sau 7, abinda zai shafi kimanin eka miliyan 40 na filin noma, wanda shine kashi 60 na abincin da ake nomawa a Yankin.

Kumar yace muddin ana bukatar shawo kan wanna matsala, ya zama wajibi a rage iskar da ake fitarwa wanda ke gurbata muhalli domin kare yankin daga wannan matsala.

Kasashen da rahotan ya ambato a matsayin wadanda ke tsakiyar Turai sun hada da Jamus da Faransa da Poland da Switzerland da Italia da kuma Austria.

Sauran sun hada da Jamhuriyar Czech da Belgium da Slovenia da Hungary da kuma Slovakia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.