Kasashen duniya sun taimakawa Lebanon da Dala miliyan 250

Shugagaban Faransa Emmanuel Macron yayin kaddamar da gidauniyar taimakawa kasar Lebanon ta hoton bidiyo
Shugagaban Faransa Emmanuel Macron yayin kaddamar da gidauniyar taimakawa kasar Lebanon ta hoton bidiyo Christophe Simon/Reuters

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen duniya da su gaggauta taimakawa kasar Lebanon wadda ta fada cikin bala’I sakamakon fashewar da aka samu a tashar jiragen ruwan kasar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150.

Talla

Kasashen duniya da dama sun amsa kiran shugaban wajen bada taimakon jinkai da ya kai Dala miliyan 250 domin taimakawa al’ummar kasar da yanzu haka suke cikin halin kakanikayi.

Majalisar Dinkin Duniya tace ana bukatar akalla Dala miliyan 117 domin amfani da su a cikin watanni 3 masu zuwa domin kula da lafiya, samar da matsugunai, rarraba abinci da kuma taimakawa jama’ar kasar.

Kungiyar kasashen Turai ta sanar da agajin euro miliyan 30 bayan euro 33 da ta sanar a baya, sai Qatar da tayi alkawarin bada Dala miliyan 50, yayin da Kuwait tayi alkawarin agajin dala miliyan 40.

Kasar Amurka tayi tayin bada agajin Dala miliyan 15, Birtaniya ta bada Dala miliyan 26, sai kuma Spain da zata bada alkalam tan 10,000.

Sauran wadanda suka bada agaji sun hada da Norway mai euro miliyan 6 da rabi, Denmark euro miliyan 20, Switzerland sama euro miliyan 3 da rabi Cyprus euro miliyan 5, Brazil tan 4,000 na shinkafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.