Wasu 'yan wasan Atletico Madrid sun kamu da korona

'Yan wasan Atletico Madrid
'Yan wasan Atletico Madrid REUTERS / Sergio Perez

Kungiyar Atletico Madrid tace wasu ‘yan wasanta biyu da bata bayyana sunansu ba sun kamu da coronavirus gabanin wasan gaf da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai, da zata kara ranar Alhamis da RB Leipzig a Lisbon.

Talla

A ranar Asabar akayiwa tawagar ‘yan wasan farko da sauran ma’aikata da zasu halarci gasar na zakarun Turai gwajin korona, kamar yadda hukumar UEFA ta tsara kafin halartan wasannin na Quarter-Finals, kuma yanzu haka ‘yan wasan biyu na killace a gida, kamar yadda kungiyar ta Spain ta fitar cikin wata sanarwa.

Club din yace, ya sanar da hukumar EEFA da hukumomin kwallon kafar Spain da Portugal da kuma hukumomin kiwon lafiya wannan lamari, kuma za’a sake sabon gwaji kan ‘yan wasan da sauran tawagar, kuma hakan na nufin jadawalin tafiyar zuwa Lisbon zai canza, to amma zasu sanar da UEFA duk wata ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.