Faransa za ta kare Faransawa a yankin Sahel - Macron

Emmanuel Macron, ici à l'Elysée le 22 juin 2020.
Emmanuel Macron, ici à l'Elysée le 22 juin 2020. Christophe PETIT TESSON / POOL / AFP

Shugabana Faransa Emmanuel Macron ya ce gwamnatinsa za ta karfafa matakan tsaro don kare Faransawa a yankin Sahel, biyo bayan kisan wasu Faransawa 6 a jamhuiyar Nijar.

Talla

Kalaman na Macron na zuwa ne a Talatar nan, kwananki biyu bayan da wasu ‘yan bindiga bisa babura suka kashe Faransawa 6 da ke yawon bude ido a yankin Kouré na jamhuriyar Nijar.

Macron ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen taimaka wa iyalan wadanda wannan aika aika ta ‘yan bindiga ta rutsa da su, kuma ba shakka za su maayar da martani ga wannan hari da ya rutsa da Faransawa 6 da ‘yan Nijar 2.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban na Faransa ya ce wadannan Faransawa da ke aiki da kungiyar agaji ta ACTED, sun nuna jajircewa wajen taimaka wa al’umma.

Saboda haka shugaba Macron ya ce ya kudiri aniyar daukar kwararan matakan tsaron rayukan ‘yan kasarsa da ke yankin Sahel, kuma zai ci gaba da aikin kakkabe kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kimanin sojin Faransa dubu 5 da dari 1 ne suke a yankin Sahel don taimaka wa dakarun hadin gwiwa na kasashe biyar na yakin a yakin da suke da ta’addanci da ya zame wa yankin karfen kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI