Dan wasan Barcelona ya kamu da korona

'Yan wasan Barcelona na kasar Spain
'Yan wasan Barcelona na kasar Spain © REUTERS/Albert Gea

Kungiyar Barcelona na kasar Spain ta ce, gwaji ya tabbatar da dan wasanta na dauke da coronavirus to sai dai bai cikin tawagar da zasuyi tafiya Lisbon domin fafata wasan daf da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai da Bayern Munich.

Talla

Klub din yace, a ranar Talata akayiwa wasu ‘yan wasa 9 da domin shirin wasanni sharan fage na kaka mai zuwa, sai gwaji ya nuna daya daga cikin su na dauke da koronan.

Barcelona tace, dan wasan baiyi wata alaka da ‘yan wasan da zasuyi tattaki zuwa Lisbon ba gobe Alhamis, tana cewa, yanzu haka dan wasan da bata bayyana sunansa ba, yana killace duk da bai nuna wani alama na rashin lafiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.