Hong Kong ta dakatar da aiki da yarjejeniyar mika masu laifi tsakaninta da Turai

Mahukuntan Hong Kong sun bayyana dakatar da aiki da yarjejeniyar mika masu laifi dake tsakanin yankin da Kasashen Faransa da Jamus kwanaki bayan da Kasashen biyu na Turai suka dau makamancin wannan mataki domin nuna adawarsu da koma bayan da aka samu na ‘yancin dan adam a birnin na Hong Kong.

Shugabar gwamntin yankin Hong Kong, Carie Lam
Shugabar gwamntin yankin Hong Kong, Carie Lam Anthony WALLACE / AFP
Talla

Sanarwar da gwamnatin Hong Kong ta fitar na cewa Faransa da Jamus sun siyasantar da yarjejeniyar dake tsakanin yankin da Kasashen biyu, abinda ke gurguntar da hadin kai ta fuskar shari’a tsakanin ita kanta Hong Kong da Faransa da kuma Jamus.

A farkon watan Agustan nan da muke ciki, ma’aikatar kula da harkokin Kasashen waje ta Faransa, ta bayyana cewa idan aka kwatanta zamanin mulkin mallakar Birtaniya da abinda ke faruwa a halin yanzu, Faransa tayi watsi da yarjejeniyar mika masu laifi, wanda a ranar 4 ga watan mayun shekarar 2017 da ta gabata aka sanya hannu a kai tsakanin Faransa da Hong Kong mai kwarya-kwaryar ‘yancin kai.

Kafin Faransa da Jamus su bayyana daukar wannan mataki dai, Kasashe da dama daga yammacin duniya kamar Canada da Amurka da Australia da kuma New zealand sun sanar da daukar mataki makamancin haka a matsayin martani ga dokar tsaro da a ranar 30 ga watan yunin da ya gabata ta soma aiki a wannan yanki, dan dakile ayyukan ta’addanci da neman ballewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI