Belarus

'Yan Belarus sun sha alwashin tilastawa Lukashenko yin murabus

Bangaren mata zalla a birnin Minsk dake zanga-zangar adawa da shugaban Belarus Alexander Lukashenko. 12/8/2020.
Bangaren mata zalla a birnin Minsk dake zanga-zangar adawa da shugaban Belarus Alexander Lukashenko. 12/8/2020. REUTERS/Vasily Fedosenko

Dubban ‘yan kasar Belarus sun ci gaba da zanga-zangar neman murabus din shugabansu Alexander Lukashenko, a daidai lokacin da shugaban ya nemi agajin takwaransa na Rasha Vladimir Putin, wajen kawo karshen rikicin siyasar dake barazanar rusa gwamnatinsa.

Talla

Yanzu haka dai dubun dubatar jama’ar da suka yi watsi da nasarar tazarcen da shugaba Lukashenko yayi, sun sha alwashin gudanar wata gagarumar zanga-zangar yau lahadi, a Minsk, babban birnin kasar ta Belarus, bayan wadda suka yi a jiya asabar.

Kawo yanzu jami’an tsaro sun kame sama da mutane dubu 6 da 700, yayinda daruruwa daga cikin masu zanga-zangar suka jikkata.

A baya bayan nan shugaban kasar  ta Belarus Alexender Lukashenko yayi watsi da tayin kasashen waje na kokarin sulhunta rikicin siyasar kasar, inda ‘yan adawa ke neman tilasta masa yin murabus.

Yayin ganawa da manyan hafsoshin tsaronsa a yau asabar, Lukashenko ya sha alwashin cewar ba zai baiwa kasashen waje damar tsoma baki a lamuransu na cikin gida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.