Faransa-Macron

Macron ya nemi sabunta tattaunawar zaman lafiyar gabas ta tsakiya

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da sabon Firaministan kasar Jean Castex.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da sabon Firaministan kasar Jean Castex. Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci a gudanar da sabuwar tattaunawar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, bayan da Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa suka kulla wata sabuwar dangantakar Diflomasiya da ke ci gaba da fuskantar mummunar suka daga Falasdinawa ko da ya ke ta samu yabawa daga kasashen yammacin Turai. 

Talla

Emmanuel Macron wanda ke bayyana hakan ta shafinsa na Twitter, bayan tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya bayyana aniyar aiki tukuru don samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Macron ya kara da cewa, yana da mutukar muhimmaci a samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya ta hanyar tattaunawa tare da mutunta dokokin kasa-da-kasa.

Shugaban na Faransa ya yaba da yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump sanar ranar alhamis, a matsayin shawara muhimmiya da hadaddiyar Daular Larabawa ta dauka, wanda ya ce alama ce, da ke nuna mahukuntan Dubai na bukatar dawwamammen zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Ya zuwa yanzu babu karin haske dangane da shirin Isra’ila na mamaye matsugunan yahudawa, da ke yamma da Kogin Jodan, duk da cewar Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce, an dakatar da shirin, bayan yarjejeniyar ta da Isra’ila

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.