Faransa

Mutum dubu 74 na neman hakkin zakaran da aka yi wa kisan gilla a Faransa

Yanzu haka dai Kotu na shirin fara zaman sauraron shari’ar a watan Disamba mai zuwa.
Yanzu haka dai Kotu na shirin fara zaman sauraron shari’ar a watan Disamba mai zuwa. Fuente: AFP.

Mutane fiye da dubu 74 ne suka sanya hannu kan takaddar shigar da karar neman adalci ga wani zakara da aka yiwa kisan gilla a Faransa, batun da ke zuwa bayan nasarar da masu goyon bayan zakaran suka samu a bara lokacin da wasu suka shigar da karar bukatar hana shi cara.

Talla

Zakaran wanda aka yiwa lakabi da Marcel mai dimbin magoya baya a kasar ta Faransa, akalla mutum dubu 74 da 500 ne suka sanya hannu kan takaddar karar ta Intanet wadda ke neman hukunta wani mazaunin kauyen Vinzieux da yi masa kisan gilla.

Tun farko mai zakaran Sebastien Verney shi ne ya fara shigar da karar bayan da wani makwabcinsa ya amsa cewa shi ya harbe zakaran har lahira tun cikin watan Mayu, batun da ya harzuka mazauna kauyen Vinzieux mai magidanta 450 a kudancin kasar.

An dai yiwa takardar karar lakabi da ‘‘Adalci ga Marcel’’ inda masu shigar da karar ke neman tuhumar makashin zakaran da cin zarafin dabbobi baya ga amfani da makami ba bisa ka’ida ba.

Masu goyon bayan zakara Marcel dai na kallon shi a matsayin wani abin kayatarwa da ke sanya nishadi a zukatan jama’a baya ga kasancewar zakara a matsayin tambari ga Faransar musamman ga tawagar kwallon kafar kasar da ta kwallon Rugby.

Yanzu haka dai Kotu na shirin fara zaman sauraron shari’ar a watan Disamba mai zuwa.

Ko a bara ma sai da magoya bayan zakaran suka tafka shari’a da wadanda basa goyon bayan wanzuwarsa kan yadda cararsa ke damunsu amma kuma zakaran ya yi nasara a gaban alkali, amma kuma zakara Marcel ya yi nasarar da ta bashi damar ci gaba da cararsa gabanin yi masa kisan gilla a watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.