Turai

Belarus: Lukashenko ya gindaya sharadi kafin mika mulki

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko REUTERS/Vasily Fedosenko

Shugaban Belarus Alexandre Lukashenko ya ce, a shirye yake ya mika mulki bayan gudanar da sabon zaben raba gardama domin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, matakin da ya dauka da zummar tausasa masu zanga-zangar adawa da sake darewarsa kan kujerar shugabancin kasar.

Talla

Sai dai shugaba Lukashenko ya ce bukatar ba za ta tabbata ba muddin yana ci gaba da fuskantar matsin lamba daga masu zanga-zanga bayan jagorar ‘yan adawar kasar, Sviatlana Tsikhanouskaya ta ce, a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar.

A yayin gabatar da jawabi, Lukashenko ya yi ta shan caccaka daga masu boren da ke fada masa cewa, ya sauka daga karagar mulki.

Sai dai Lukashenko ya ce, ba za a sake gudanar da wani sabon zaben shugaban kasa har sai an kashe shi, amma ya yi tayin gudanar da zaben raba gardama domin sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Wasu da dama dai na ganin wannan tayin nasa ba zai tausasa masu zanga-zangar ba, da ke cewa, ya sha fadin makamancin wannan batu a can baya.

A cewar shugaban na Belarus, zai mika karfin ikonsa da zarar an gudanar da zaben raba gardama don yi wa kundin tsarin mulkin gyarar fuska, amma ba a karkashin matsin lamba ba.

Yanzu haka dai, shugaban na fuskantar barazanar takunkumai daga Kungiyar Tarayyar Turai sakamakon murkushe masu boren da ke adawa da sake zabensa a makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.