Birtaniya

An karkare taron Birtaniya da EU karo na 7 ba tare da cimma jituwar kasuwanci ba

Manyan masu shiga tsakani na bangaren Birtaniya da EU kan tattaunawar kasuwanci Michel Barnier da David Frost.
Manyan masu shiga tsakani na bangaren Birtaniya da EU kan tattaunawar kasuwanci Michel Barnier da David Frost. Oliver Hoslet/Pool via REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai ta koka da rashin ci gaban da ake samu a tattaunawarta da Birtaniya kan yadda kasuwancinsu zai ci gaba da gudana bayan karewar wa’adin ficewar kasar.

Talla

Babban mai shiga tsakani kan tattaunawar Birtaniya na kungiyar EU Michel Barnier a gargadin da ya gabatar bayan kawo karshen tattaunawa karo ta 7 wadda ita ma ba a kai ga cimma nasara ba, ya ce abin takaici ne yadda aka gaza cimma daidaito.

Daruruwan masu shiga tsakani ne suka hallara a Brussels cikin makon nan, da nufin kawo karshen tattaunawar kan alakar kasuwancin bangarorin biyu, amma kuma batutuwa masu alaka da dokokin suu dana alakar kamfanoni.

Cikin bayanan Michel Barnier ya ce ko shakka babu mahalarta taron da shi kansa basu gamsu da abin da ya faro a ganawar wadda ta kawo karshe yau juma’a ba, yana mai cewa alamu na nuna tattaunawar bangarorin biyu na komawa baya ne maimakon ci gaba.

Sai dai wakilin Birtaniya a tattaunawar David Frost ya ce sun aminta da dukkannin bukatun da EU ta gabatar game da dokokin SUU amma sauran bukatun da ta nema ne ke da matukar wahalar amincewa.

Mr Frost ya bayyana cewa Birtaniya a shirye ta ke a gaggauta kammala tattaunawar sai dai bukatun da EU ke gabatar na da matukar tsauri kuma ba za su iya cimmuwa cikin sauki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.