Turkiya ta gano iskar gas makare a gabar tekun Black Sea
Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan, ya ce kasar ta gano wani katafaren fili da ke gabar tekun Black Sea makare da iskar gas, kuma nan ba da jimawa ba kasar za ta fara aikin hako shi.
Wallafawa ranar:
Shugaba Racep Erdogan ya ce iskas gas da aka gano zai kai akalla cubic mita bilyan 320 bayan fara aikin bincike da injinoyoyin kasar suka fara a cikin watan jiya.
Erdogan ya ce a shekara ta 2023 lokacin da al’ummar kasar ke murnar cika shekaru 100 cur da kasar da zama sabuwar jamhuriyar irin ta zamani, domin kaddamar da bututun iskar gas na farko domin amfanin al’umma.
Turkiyya dai ta yi amfani da wani katafaren jirgin ruwan bincike Ottoman Sultan Fatih Mehmet da ke nufin sunan wanda ya kafa kasar Turkiyya a shekara ta 1453 domin gudanar da wannan bincike.
A tsawon shekaru dai, Turkiyya dai ta dogara ne da Rasha domin samun iskar gas da take amfani da shi a cikin gida, to sai dai inda kasar ke cewa ta gano wannan iskar gas, yanki ne da ake takaddama tsakanin Turkiyya da kuma Girka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu