Amurka

Gobarar daji ta kone fadin kasa sama da kadada dubu 220 a California

Yadda gobarar daji ta ratsa yankin Shasta dake jihar California, a Amurka. 6/9/2018
Yadda gobarar daji ta ratsa yankin Shasta dake jihar California, a Amurka. 6/9/2018 CALIFORNIA HIGHWAY PATROL/via REUTERS

Hukumomin jihar California a Amurka sun ce wutar daji na cigaba da mamaye dazukan yankin, inda kawo yanzu ta kone fadin kasar da ya zarta dubu 220, da kuma kone gine-ginen kusan 500.

Talla

Jami’an kwankwana sun ce kawo yanzu mutane 7 suka rasa rayukansu, a dalilin gobarar dajin da suka ce saukar tsawa sama da sau dubu 12 ya haddasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Masana sun bayyana gobarar dajin da ta tashi tun tsakiyar ranar litinin da ta gabata, a matsayin irinta ta 10 mafi muni da aka gani a jihar California.

Zuwa yanzu kimanin mutane dubu 119,000 gobarar dajin ta tilasta tserewa daga daga muhallansu, yayinda jami’an kwana-kwana suka ci kashi 7 cikin 100 kawai suka iya kashewa na gobarar dajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.