Rasha

Jagoran 'yan adawar Rasha da ake zargin an dirkawa guba ya isa Jamus

Asibitin birnin Omsk, da aka soma kwantar da Alexeï Navalny kafin fita da shi zuwa kasar Jamus.
Asibitin birnin Omsk, da aka soma kwantar da Alexeï Navalny kafin fita da shi zuwa kasar Jamus. REUTERS/Alexey Malgavko

Bayan shafe kwana guda ana cece-kuce kan lafiyarsa, yau asabar jami’an lafiya daga birnin Omsk sun isa birnin Berlin na Jamus da jagoran ‘yan adawar Rasha Alexie Navalny domin samun karin kulawa kan rashin lafiyar da ta janyo masa dogon suman da har yanzu bai farfado ba tun a ranar Alhamis.

Talla

Da fari likitocin da suka soma kula da Navalny a garin Omsk sun ki bari a fita da shi, domin a cewarsu jikinsa yayi tsananin da ba za a iya fitar da shi zuwa wani asibitin ba, abinda ya sanya iyalai da sauran ‘yan adawa zargin cewar ana neman jefa rayuwarsa ne cikin hadari da gangan, tare da zargin guba aka shayar da shi, zargin da likitocin suka musanta.

Wasu na hannun daman jagoran ‘yan adawar na Rasha na cigaba da nanata cewar guba aka shayar da shi, ta hanyar sanya mishi ita a shayin da ya sha kafin yin balaguro daga filin jiragfen sama na garin Tomsk dake lardin Siberia, inda ya halarci taron gangamin ‘yan adawa kan zabukan yankunan dake tafe a shekara mai zuwa.

Shugabannin kasashe da dama ciki har da Angela Merkel ta Jamus da Emmanuel Macron na Faransa sun bayyana damuwa kan halin da Navalny ke fuskanta, a tsawon sama da shekaru 10 da ya shafe yana adawa da shugaban Rasha Vladmir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.