Amurka

California ta nemi agajin makwafta kan gobarar dajin da ta addabe ta

Wani jami'in kwan kwana yayin kokarin baiwa wani gida kariya daga gobarar dajin da ta addabi sassan jihar California. 21/8/2020.
Wani jami'in kwan kwana yayin kokarin baiwa wani gida kariya daga gobarar dajin da ta addabi sassan jihar California. 21/8/2020. REUTERS/Stephen Lam

Jihar California dake Amurka ta nemi agajin makwaftanta, sakamakon yadda gobarar daji kashi kusan 30 ke cigaba da kone sassanta.

Talla

Ma’aikatar lura da gandun dajin jihar ta ce tsananin zafi da kuma tsawa ne ke cigaba da haddasa gobarar da zuwa yanzu babu alamun samun nasarar shawo kanta, bayan kone fadin kasar da ya zarce kadada dubu 400, da kuma kone wasu gine-gine kusan 700.

Yanzu haka dai kusan ‘yan kwanakwana dubu 14 ke fafutukar kashe gobarar da ta tilastawa kimanin mutane dubu 175 tserewa daga gidajensu.

Jami’an agaji sun ce mutane 7 sun rasa rayukansu, yayinda wasu 43 ciki harda jami’an kwanakwana sun jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.