Amurka-Trump

Trump ya tura dakaru don kwantar da tarzomar masu zanga zanga

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tura Karin jami’an tsaro zuwa Kenosha dake Winconsin dan ganin sun kwantar da zanga zangar da tayi sanadiyar kasha mutane 2 dake nuna bacin ran su da harbin da Yan Sanda suka yiwa James Blake.

Talla

Shugaban yace ba zasu zuba ido suna kallo ana sata da kona dukiya da kuma tashin hankali ba a titunan Amurka, saboda haka ya bada umurnin tura dakarun kasa domin mayar da doka da oda.

Trump ya sanar da haka ne bayan ya tattauna da Gwamnan Winconsin Tony Evers inda yake cewa ya zama dole a dawo da doka da oda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.