Sufuri

COVID-19: Ma'aikatan kamfanonin jiragen sama kusan dubu 90 za su rasa aiki

Tasirin annobar coronavirus na barazanar raba dubban ma'aikatan kamfanonin sufurin jiragen sama da guraben ayyukansu.
Tasirin annobar coronavirus na barazanar raba dubban ma'aikatan kamfanonin sufurin jiragen sama da guraben ayyukansu. REUTERS/NICK OXFORD

American Airlines, kamfanin sufurin jiragen sama na Amurka, ya ce zai sallami ma’aikatansa dubu 19, 000 a cikin watan Oktoba dake tafe, lokacin da shirin gwamnati na baiwa kamfanonin sufurin jiragen sama tallafin kudade don rage radadin tasirin annobar COVID-19 zai kawo karshe.

Talla

Kamfanin sufurin jiragen na Amurka dake kan gaba a duniya, yace sallamar ma’aikatan zai sanya yawan hadiman nasa raguwa zuwa kashi 30 cikin dari.

Tuni dai wasu manyan kamfanonin sufurin jiragen saman suka yi gargadin yiwuwar sallamar dubban ma’aikatansu, duk saboda tasirin annobar coronavirus.

Kamfanonin kuwa sun hada da United Airlines da shi ma ke Amurka, wanda a watan Yuli yace ma’aikatansa dubu 36 ke cikin hadarin rasa ayyukansu. Sai kamfanin Luftansa na Jamus da shi kuma ya ce mai yiwuwa ya sallami ma’aikatansa dubu 22, 000, yayin da na British Airways ya sanar shirin rage ma’aikata dubu 12, 000.

Shirin rage dubban ma’aikatan da kamfanonin sufurin jiragen ke yin a zuwa ne, yayinda masana suka yi hasashen fannin sufurin jiragen sama na kasashen duniya, zai tafka hasarar sama da dala biliyan 84 a shekarar bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.