Jamus-Turkiya

Jamus ta bukaci Turkiya da Girka su kai zuciya nesa kan rikicinsu

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Hayoung JEON / POOL / AFP

Jamus ta bukaci kasashen Turkiya da Girka su kawo karshen atisayen Sojin ruwan da su ke ci gaba da yi yanzu haka sakamakon takaddamar da ke kara tsami tsakanin kasashen biyu dangane da batun iyakar ruwa da albarkatun iskar gas da aka gano a Mediterranean.

Talla

Kiran na Jamus na zuwa ne bayan taron ministocin wajen kasashen EU a Berlin da suka yi tattaunawa ta musamman kan fargabar yiwuwar barkewar yaki tsakanin kasashen 2 da ke ci gaba da takun saka dai dai lokacin da ‘yan korar Girka ciki har da Faransa Italy da Cyprus ke mara baya ga atisayen.

Duk dai a yau Alhamis din Turkiya ta sanar da kara yawan dakarun da ke atisayen Sojin a karshen iaykarta ta ruwa da ke kusurwar arewa maso gabashin tekun mediterranean yankin kasashen ke ci gaba da takaddama a kansa.

Sai dai Jamus wadda ke kokarin shiga tsakanin kasashen biyu, ta bakin ministan harkokin wajenta Heiko Maas ta bayyana bukatar warware rikicin ta fuskar Diflomasiyya tun kafin ya tsananta.

A cewar Jamus ko shakka babu kasashen biyu baza su aminta da zama kan teburin sulhu dai dai lokacin da jiragen yakinsu ke fuskantar juna a iyakar ruwansu ta tekun Mediterranean.

Tun kafin yanzu dai EU ta nuna matukar damuwa da yadda Turkiya ta girke Sojin ruwan dama kawar da kan da ta yi game da kiraye-kirayen da ake mata game da aikin hakar gas din da ta gano makare a yankin da kungiyar ke ikirarin ba mallakin Turkiyan ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.