Amurka

Trump ya aike da karin jami'an tsaro zuwa Kenosha don murkushe masu bore

Masu zanga-zanga a garin Kenosha dake Wisconsin kan harbin da 'yan sanda suka yiwa wani bakar fata.
Masu zanga-zanga a garin Kenosha dake Wisconsin kan harbin da 'yan sanda suka yiwa wani bakar fata. AP/David Goldman

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tura karin jami’an tsaro zuwa Kenosha dake Wisconsin, dan ganin sun kwantar da zanga-zangar da tayi sanadin kashe mutane 2 dake nuna bacin ransu da harbin da ‘yan sanda suka yiwa James Blake.

Talla

Shugaban yace ba zasu zuba ido suna kallo ana sata da kona dukiya da kuma tashin hankali ba a titunan Amurka, saboda haka ya bada umurnin tura dakarun kasa domin mayar da doka da oda.

Trump ya sanar da haka ne bayan ya tattaunawa da Gwamnan Wisconsin Tony Evers, inda yake cewa ya zama dole a dawo da doka da oda.

A baya bayan nan, hukumar dake shirya gasar kwallon kwando a Amurka NBA ta sanar da dage dukkanin wasanni 3 na sharar fage da aka tsara za su gudana har zuwa wani lokaci da kawo yanzu bata bayyana ba.

NBA ta dauki matakin ne bayan da kungiyar kwallon kwando ta Milwaukee Bucks ta kauracewa wasan da za ta fafata da Orlando Magic, don nuna bacin rai kan harbin da ‘yan sandan suka yiwa bakar fata, abinda ya kai ga haddasa masa mutuwar barin jiki, a ranar talatar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.