Faransa

COVID-19: Sanya takunkumin rufe fuska ya zama tilas a Faransa

Fira Ministan Faransa Jean Castex tare da ministan tattalin arzikin Faransa Bruno Le Maire. 26/8/2020.
Fira Ministan Faransa Jean Castex tare da ministan tattalin arzikin Faransa Bruno Le Maire. 26/8/2020. Charles Platiau/Reuters

Gwamnatin Faransa ta tilasta amfani da takunkumin rufe baki da hanci a ilahirin birnin Paris daga yau Juma’a, sakamakon yadda annobar coronavirus ke kara bazuwa tsakanin al’umma.

Talla

Fira ministan Faransa Jean Castex, ya bayyana daukar matakin, inda ya bukaci al’umma da ta taimaka wajen hana yaduwar cutar.

Castex ya bayyana sanya karin kananan hukumomin Paris guda 19 cikin taswirar masu alamar Ja, ma’ana yankunan masu barazanar saurin yaduwar annobar ta COVID-19, wanda ke nufin 21 daga cikin 94 na kananan hukumomin Paris ke tattare da hadarin sake bazuwar annobar.

Yanzu haka cutar na kara bazuwa a Faransa, abinda yasa mahukunta ke fargabar sake barkewar ta a karo na biyu, la’akari da cewar ko a jiya Alhamis, an gano sabbin wadanda suka harbu da annobar ta COVID-19 har dubu 4 da 500 cikin sa’o’i 24 a kasar at Faransa, ciki harda wadanda aka kwantar a sashin gaggawa na asibitoci.

Dama dai wajibi amfani da Kellen na rufe hanci da baki a motocin sufuri da bainar jama’a a duk fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.