Faransa

Shugaban Faransa ya haramta amfani da danko wajen farautar tsuntsaye

Ire-iren tsuntsayen da mafarauta ke kamawa ta hanyar amfani da danko a Turai.
Ire-iren tsuntsayen da mafarauta ke kamawa ta hanyar amfani da danko a Turai. © Felix Kaestle/AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bada umurnin haramta amfani da danko ko kuma gum, wajen farautar tsuntsaye.

Talla

Fadar shugaban kasar tace shugaba Macron ya bada umurnin dakatar da farautar ta wannan hanyar ce har zuwa lokacin da kotun Turai zata yanke hukunci kan karar da aka shigar dangane da salon farautar.

Masu kare muhalli suka gabatar da karar inda suka ce salon farautar amfani da dankon na janyo mutuwar tsuntsaye akalla 150,000 ta irin wannan hanyar, abinda kungiyar kasashen Turai ta bayyana a matsayin azabtarwa.

Cikin watan Yuli kungiyar EU ta bukaci Faransa da ta sake nazarin damar amfani da gum ko danko da aka baiwa masu farautar tsuntsaye a kasar, wadda ke zama ta karshe a yammacin turai da mafarautar ke amfani da wannan salo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.