Coronavirus

Faransa: Sama da mutane dubu 7 sun kamu da coronavirus a kwana 1

Mutane sanye da takunkuman rufe baki da hanci a birnin Nantes dake Faransa. 24/8/2020.
Mutane sanye da takunkuman rufe baki da hanci a birnin Nantes dake Faransa. 24/8/2020. © REUTERS - Stephane Mahe

Ma’aikatar lafiyar Faransa tace an gano karin mutane dubu 7 da 379 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar cikin sa’o’I 24, adadi mafi yawa tun bayan wanda aka gani kafin janye dokar hana jama’a zirga-zirga a watannin baya.

Talla

Kadan ya rage adadin sabbin kamuwa da cutar ta coronavirus na ranar ta Juma’a ya gaza kaiwa irin wanda aka gani a Faransar ranar 31 ga watan Maris, lokacin da annobar ta kai matakin kololuwa, inda mutane dubu 7 da 578 suka kamu da cutar a kwana guda.

Sake yaduwar annobar ta coronavirus ya sanya tunanin yiwuwar gwamnatin faransa ta sake killace jama’a, to sai dai shugaba Macron bai yi na’am da shawarar ba.

Yanayin na zuwa ne yayinda dalibai ke shirin komawa makarantu nan da ‘yan kwanaki, karo na farko tun bayan dakatar da karatun cikin watan Maris.

A wannan Juma’ar dokar tilastawa jama’a sanya takunkumin rufe baki da hanci ta soma aiki a daukacin Faransa, domin dakile annobar dake neman komawa sabuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.