Barazanar ta'addanci na kara girma a Faransa - Minista

Asumiyar Eiffel da tutar Faransa
Asumiyar Eiffel da tutar Faransa Ludovic Marin / AFP

Gamnatin Faransa tace, har yanzu barazanar ayyukan ta'addanci a kasar na da girman gaske, bayan da kundin ragistan masu tsatsauran ra’ayin islama a kasar ya nuna fiye da mutum dubu 8.

Talla

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai Chelkwatan tsaron kasar, Litinin din nan, inda aka nuna masa kundin da ke dauke da sunayen mutane da jami’an tsaro ke bibiyar su a matsayin masu tsatsauran ra’ayin addinin musulunci, har dubu 8132.

Ministan yace, hakan na tabbatar da girman da barazanar hare-haren ta’addanci da kasar ke fuskanta yanzu haka, to sai dai yace, gwamnati bazatayi kasa aguiwa ba, wajen kare al’umma daga wannan barazana.

Mista Darmanin ya yabawa jami’an tsaron cikin gida masamman masu tara bayanan sirri da ke tsinto masu tsatsauran ra’ayin addini a duk inda suke, ya kuma shaida karin sabbin jami’an tsaro 1260 da za’a dauka kwanan nan.

Wannan na zuwa ne kwanaki 2 kafin soma shari’ar wadanda ake zargi da taimakawa wadanda suka kitsa harin ta’addanci kan ofishin mujallar nan ta barkwanci Charlie Hebdo, dake birnin Paris, a shekarar 2015, harin da yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.